• Mutun Sha hudu masu Garkuwa su ka tafi da su, Amma an ce to mutun biyu, bayan gunduna ta musamman ta Kai dauki.
• Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Kachia.
• Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.
Rundunar yan sandan jihar Kaduna, ta tabbatar da garkuwa da mutane goma sha biyu, a wani sabon hari da aka kai jihar.
An dai bayyana cewa, Maharan sun kai harin ne, a ranar Laraban data gabata, a yankin Awon/Mothercat na karamar hukumar Kachia dake jihar, inda su ka yi garkuwa da mutane.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mohammed Jalige ne ya tabbatar da afkuwar lamarin a Kaduna, inda ya ce, an kuma ceto mutun biyu, daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
A cewar sa, Maharan sun afka yankin ne da misali karfe 9 da minti 20 na dare, inda suka fara harbi Kan me uwa da wabi ga mazauna yankin, dake kan gudanar da harkokin su na yau da kullun.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ansaki sarki da matar shi bayan anyi garkuwa dasu
“Bayan samun bayanai kan lamarin ne, rundunar hadin gwaiwa da ta hadar da jami’an soji, yan sanda da kuma na yan sankai, su kayi hanzarin isa yankin domin Kai dauki, inda suka raunata batagari 4 da kuma kashe 1 daga ciki” inji shi.
Ya ce, sai dai mutun goma sha hudu cikin mutanen yankin sun sami raunuka lokacin harin yan bindiga, inda a ka kai su asibiti mafi kusa domin duba lafiyar su cikin gaggawa.
A karshe Jalige ya ce, “Rundunar yan sandan jihar ta na sake jajantawa yan uwa da kuma ilayan wadanda lamarin ya shafa, inda kuma ta ke fatan samun sauki cikin gaggawa, ga wadanda suka sami raunuka” inji shi.