An yi garkuwa da shugaban karamar hukumar Kanke ta jihar Filato, Honarabul Henry Gotip.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, An ce an yi garkuwa da shi ne da misalin karfe 1 na dare wayewar garin Laraba.
Karanta kuma: An Yi Garkuwa da Mutum 4 a Jihar Kogi
Wata majiya ta shaida wa Daily trust cewa da sanyin safiyar Laraba ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan Shugaban karamar Hukumar da ke Kwang a karamar hukumar Jos ta Arewa, inda suka yi awon gaba da shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, da aka tuntube shi kan lamarin, ya ce zai kira wakilinmu da zarar ya samu cikakken bayani kan lamarin.
A wani labarin kuma: Wike Bai Halarci Ganawar Atiku Da Yan Takarar Shugaban Ƙasa Ba
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci wani taro ba a ranar Laraba a lokacin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da masu neman takarar shugabancin jam’iyyar a 2023 a gidansa da ke Asokoro a Abuja.
Baya ga Wike, akwai kuma tsoffin shugabannin majalisar dattawa Bukola Saraki da Pius Anyim da kuma gwamna Emmanuel Udom na jihar Akwa Ibom.