By Abbas Yakubu Yaura
An yi garkuwa da wasu masu yiwa kasa shidima na NYSC guda biyu daga jihar Benue zuwa Kebbi da Sokoto a hanyar Tsafe zuwa Gusau ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Talata lokacin da ‘yan fashin suka tare motar mai lamba GBK 339 ZY dake dauke da ‘yan yi wa kasa hidima.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Juma’a, yace ‘yan bautar kasa guda biyu suna cikin sauran wadanda abin ya shafa (wanda har yanzu ba a san su ba) wadanda da aka sace.
SP Shehu yace shugaban gudanarwar NYSC na jihar ne ya kai rahoton lamarin ga rundunar ‘yan sanda, A cewarsa, “Rahoton da rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta samu daga gareshi NYSC na jihar ya nuna cewa, mutum biyu (2) masu yiwa kasa hidima da aka tura daga jihar Binuwai zuwa Jihohin Kebbi da Sokoto na cikin wadanda aka sace a hanyar Tsafe zuwa Gusau a ranar Talata 19 ga watan Oktoba, 2021 da misalin awanni 2230.
“An samu rahoton da safiyar Juma’a lokacin da Kwamishinan‘ yan sanda CP Ayuba N. Elkanah ya ziyarci sansanin Gabatarwa dake Tsafe don tantance matsugunin tsaro da ake da shi a sansanin wayar da kai da nufin tabbatar da tsaro da amincin membobin Rundunar.
“Kazalika, ana ci gaba da aikin gudanar da ceton don tabbatar da kubutar da membobin kungiyar tare da sauran wadanda aka sace.
“Kwamishinan a cikin jawabinsa ga membobin dake shirin zuwa aikin yiwa kasa hidima ya tabbatar musu da karin himma na ‘yan sanda don kare rayuwarsu tare da umartar su da su kasance masu kula da tsaro, ”in ji SP Shehu.