Wani yamutsi ya barke a zauren majalisar jihar Bayelsa. Yamutsin da ya auku a zauren majalisar jihar ne ya yi sanadin sanar da wani Kakaki bayan arcewar da mai rike da mukamin ya yi a wannan Litinin.
Rahotanni daga Bayelsa da ke yankin kudancin Nijeriya, na cewa an ji karar harbe-harbe a majalisar dokokin jihar bayan wani yamutsi da aka samu lokacin da ake kokarin tsige kakakin majalisar.
Jami’an tsaro ne dai suka yi ta harbe-harben a cewar rahotannin, sakamakon tsananin rudanin da ya kaure a zauren majalisar a wannan Litinin.
Wani ganau ya shaida wa wakilin DW Hausa na yankin Neja Delta a Nijeriya, Muhammad Bello cewar ‘yan majalisar na kokarin tsige kakakin majalisar ne ya haddasa harbe-harben.
Koda yake Kakakin majalisar da za a tsige din ya arce da sandar majalisar, ‘yan majalisar sun tsige shi sun dora sabo, a cewarsa.