A yau Talatar ne aka bizne George Floyd da mutuwarsa ta haifar da zanga-zangar nuna adawa da zalunci da cin zarafin mutane masu launi da jami’an tsaron Amurka ke ci gaba da yi.
A Amurka, a yau Talata aka yi jana’izar George Floyd, mutumin da mutuwarsa ta janyo zanga-zanga a cikin Amurka da wasu sassan kasashen duniya.
An binne dan shekara 46 din ne a kusa da mahaifiyarsa a wata makabartar da ke birnin Houston inda Marigayin ya girma.
A daya bangaren kotu ta nemi dan sandan da ya yi ajalinsa da ya biya kudin beli na Dala miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin.