A yau Asabar 2 ga watan Janairun 2021 da misalin karfe 10:00 na safe aka gabatar da sallar jana’izar Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu wanda ya rasu a ranar Juma’a.
Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarta. An gabatar da jana’izar ne a Babban Masallacin Juma’a na Kwata dake Sabon garin Zariya.
Babban Limamin Zazzau ne ya jagoranta.