Shu’aibu Ibrahim Gusau
Anyi kira ga ladanan masallatan Juma’a dake jihar zamfara dasu tashi su nemi ilimin addini, musamman na kiran sallah .
Wannan kiran ya fitone daga bakin uban kasar tudun wada Alhaji Nuraddeen kabir Danbaba, a lokacin da ya zanta da wakilinmu a wurin taron kungiyar ladanan juma’a na cikarsu shekara daya da kafawa a jihar zamfara.
Uban kasar na tudun wada ya kara da cewa ba’a kiran sallah da jahilci, dolene a nemi ilimi akanshi don sanin yadda ya kamata a kira sallah.
Kuma ya bukaci ladanan dasu rika biyayya ga malamansu da kuma shuwagabanninsu.
Daya yake tofa albarkacin bakinsa a wurin taron kuma wakilin gwamnatin jihar zamfara a wurin taron, sakataren gwamnatin jihar zamfara Farfesa Abdullahi Muhammad walin shinkafi .
Ya bayyana cewa lalle su ladanan sunyi tunani da suka kafa wannan kungiya a wannan jihar, domin a cewarsa babu bangaren da basuda kungiya, kamar kungiyar limamai dana Na’ibai dana kabu kabu da dai sauransu,don haka ya bukaci kungiyar su zama masu hakuri da biyayya.
Taron dai ya sami halartar malamai daban daban wadanda suka ja hankali tare da Jan hankalin ladanan don sanin yadda zasu rika kiran sallah a kodawane lokaci .