Dakarun rundunar hadin gwiwa ta kasa da kasa (MNJTF), sun kashe wani babban jigo na kungiyar Da’ish ta Iraki da Siriya (ISIS), Ammar Bin-Umar, a yankin tafkin Chadi, a lokacin da aka kai musu hare-hare ta sama, kamar yadda wata majiyar soja ta bayyana.
Hare-haren na hadin guiwa a cewar majiyar, rundunar sojojin saman Nijeriya tare da hadin guiwar dakarun MNJTF, Mi35 da Helicopter Gunship na Mi171 na Neja suka kai harin a ranar 14 ga Afrilu, 2022 a Arinna, karamar hukumar Marte ta jihar Borno.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zaben Shugaban kasa 2023: Ba za ka yi nasara ba——- Ganduje ya fadawa Gwamna Wike
A cewar wani bayanin leken asirin da Zagazola Makama, kwararre kan yaki da ‘yan tada kayar baya ya samu, an kashe Bin-Umar ne a wani yunkurin tserewa daga tafkin Chadi, bayan wani harin sama da aka shafe tsawon mako guda ana yi.
Hukumar leken asirin a cewar rahoton, ta kai hare-haren tiyata a Kwalaram da Sabon Tumbun da Jibularam, wanda ya tilastawa kungiyoyin ta’addanci komawa tare da neman mafaka a wasu sabbin maboya a yankunan Kwalori da Doron Kirta da Buningyil da Lokon Libi a cikin tafkin Chadi.
“An kwashe ‘yan kungiyar ta ISIS da suka tsira zuwa KIRTA da misalin karfe 06:00 na safe, sannan aka kai su a cikin wasu jiragen ruwa guda biyu dauke da buhuna dauke da kudade da ake zargin ana daukar nauyin kungiyar ta ISWAP, a kokarin tserewa ta hanyar Chikka da Mardas, dukkansu a kan iyakar Kamaru.
“Bin-Umar yana daya daga cikin manyan kwamitin tattaunawa na Mujahidan ISIS da aka tura zuwa lardin Boko Haram/Islamic State West Africa Province (ISWAP), Khalifanci a watan Fabrairun 2022, don shiga tsakani sakamakon tsawaita yakin da ake yi tsakanin kungiyar Jama’at Ahl as-Sunnah. Da’awah wa’l-Jihad na bangarorin Boko Haram da ISWAP.”
Majiyar ta ce “Wakilan ISIS kuma sun zo ne domin sa ido kan kafa “Darul Quran