Shugabannin Sudan ta Kudu da ke rikici da juna sun cimma yarjejeniya game da kafa gwamnatin sojin-hadaka, biyo bayan jan-kafar da aka yi ta samu dangane da kawo karshen takun-sakarsu.
Martin Abucha, shi ne wakilin Machar da ya rattaba hannu kan yarjejejeniyar, ya kuma ya ce, zaman lafiya ya ta’allaka ne da tsaro, sannan sun cimma gaci a cewarsa.
Ministan Kula da Harkokin shugaban kasar ta Sudan ta Kudu , Barnaba Marial Benjamin ya yaba da wannan yarjejeniya wadda aka cimma bayan makwabciyarsu Sudan ta shiga tsakani don samar da masalaha.
A ‘yan kwanakin nan, an ga yadda bangarorin biyu suka yi tayar da jijiyoyin wuya, al’amarin da ya jefa fargaba a zukatan kasashen duniya kan yiwuwar sake kazancewar tashin hankali a kasar ta Sudan ta Kudu.
Shugabannin biyu, wato Kiir da Machar duk sun samu halartar bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar a birnin Juba a jiya Lahadi, inda suka amince cewa, bangaren Kiir zai samu kashi 60 na sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a kasar, yayin da bangaren Machar ke da kashi 40.