Cikin kasa da kwana guda kenan ɗan wasan Tennis din nan na kasar Birtaniya Jamie Murray ke shan kashi a wasu tagwayen wasanni da ya fata cikin gasar French Open.
Dan wasan dan kasar Birtaniya da takwaransa na Brazil Bruno Soares sun sha duka ne hannun yan kasar Romaniya Horia Tecau da kuma dan kasar Jamus Kevin Krawietz zagaye na uku cikin gasar French Open din na maza.
A hannu guda kuma Neal Skupski da Alexa Guarachi duk sun tsallake zuwa zagaye na gaba.