By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar ‘yan sandan jihar Imo ta gano wata yarinya ‘yar shekara 3 da aka yi watsi da ita a cocin St Mulumba Katolika da ke kan titin Wethedral a Owerri babban birnin jihar Imo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, PPRO, Micheal Abattam, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Owerri ranar Laraba.
A cewar ‘yan sandan, an gano karamar yarinyar kurma ce kuma da kyar ne samun cikakken bayaninta.
Rundunar ‘yan sandan ta ce: “Rundunar ‘yan sandan jihar Imo tana son sanar da jama’a game da wata yarinya da aka yi watsi da ita, wacce ba a san ta ba, mai kimanin shekaru 3 wanda ta kasance kurmace.
“An tsinci jaririyar kurma a harabar cocin St Mulumba Catholic dake kan titin Wethedral da misalin karfe 17:30 na ranar 1 ga watan Janairu, 2022 kuma duk kokarin da aka yi na gano iyayen ya ci tura.”
Sai dai rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga jama’a da za su iya sanin yarinyar ko kuma iyayen ta da su zo ofishin jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, domin tantancewa da karbarta.