Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Shakhtar ta yiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid wankan jego a wasan farko na gasar zakarun turai a wasannin rukuni a wannan yammaci na Laraba kuma a filin wasa na Santiago Barnabeau dake ƙasar Andalus.
Shakhtar ta wanke Real Madrid daci 3 da 2 inda saida Shakhtar ta fara jefa dukkanin ƙaallayen guda uku kana daga bisani Real Madrid ta rama ƙwallaye guda biyu inda akayi ta gumurzu kuma aka tashi a haka.
Wannan rashin nasara da Real Madrid tayi ana ganin ka iya zamemata barazana a wasannin na rukuni ganin yadda anan gaba zata fafata da Inter Milan da kuma Brussia M’gladbach a wasannin gaba, kuma ana ganin tabbas zasu iya sake yin tuntuɓe a wasannin na gaba.
Real Madrid dai itace tafi kowacce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ajiye tarihi a wannan gasa ta zakarun turai inda ta lashe gasar sau 13 kuma gashi ta fara da rashin nasara. Haka zalika a makon daya gabata Real Madrid tayi rashin nasara ta farko a gasar Laliga a hannun ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Cadiz daci 1 da nema.
A mako mai kamawa ne dai Real Madrid zata fafata wasan hamayya mai taken El-Clasico da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona a filin wasa na Camp Nou wasan da ake ganin idan har Real Madrid ta sake tayi rashin nasara to ta tabbata tayi rashin nasara guda uku a jere a mako ɗaya.