Shugaban Hukumar Lafiya a Matakin Farko na Kasa Faisal Shuaib, a ranar Asabar ya bayyana cewa, a halin yanzu an yiwa mutane miliyan 4,680,000 rigakafin Kurona a Nigeria.
Faisal Shuaib ya bayyana haka a Benin, a lokacin Babban taro na Kudu maso kudu akan rigakafin Kurona, wanda Kwamitin Shugaban Ƙasa akan cutar Covid-19 haɗin gwiwa da Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta ƙasa, suka shirya.
Yace an shirya taron ne domin tattaunawa akan rigakafin Kurona, magance wasu matsaloli, cimma matsaya gami da bayar da goyon baya akan ƙoƙarin da Gwamnatocin tarayya da jahohi suke yi, domin su tabbatar da cewa ƴan ƙasa sun kasance cikin ƙoshin lafiya, tare da kare su daga cutar Covid-19.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mangal ya ginawa ƴan ƙadiriyya Makarantar Islamiyya a Katsina
Shuaib ya ƙara dacewa, cikin yawan mutanen da aka ambata, kimanin mutane miliyan 1,865,127 sun karɓi maganin kashi na biyu.
Yace duk da irin nasarar da aka cimmawa, ya bayyana cewar ƙididdigar akayi tayi ƙasa da mutanen da aka shirya yi mawa rigakafin, domin kowa ya dawo gudanar da rayuwar sa yadda ya kamata.
Ya alaƙanta rashin cimma adadin mutanen da aka so yi mawa, da rashin bayanai da suka samu akan cutar da rigakafi, inda yace tunani irin nada ya kawo hakan.
“A yanzu bawai muna yaƙi da cutar Covid-19 kaɗai ba, har da rashin samun ilmi akan rigakafin cutar, wanda ya haifar da tsanar rigakafin a faɗin duniya, a yayinda cutar take cigaba da laƙume rayukan al’umma.
“Domin tabbatar da gaskiya akan rigakafin, Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko tana haɗa hannu da Hukumar kula da hana zagon ƙasa ICPC, gami da Hukumar Kula da almundahana EFCC” inji shi.
Ministan Lafiya Dr Osagie Ehanire yace a halin yanzu Nigeria ta rasa mutane dubu 2000 da suka mutu sakamakon cutar Covid-19, a yayinda ta girgiza tattalin arzikin ƙasar ya zuwa kaso 33 cikin ɗari.
Yace Gwamnatin Tarayya tana son ta yiwa kashi 70 na yawan al’ummar ta rigakafin, domin magance yaɗuwar cutar.
Shima dayake Jawabi, Gwamnan Jahar Edo Godwin Obaseki yace Jahar ta yiwa a ƙalla mutane dubu ɗari 130,000 rigakafi akan cutar.