Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta kama wani matashi dan shekara 30 mai suna Ajibola Akindele da laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara 20 fyade a cikin wani coci dake Abeokuta babban birnin jihar.
An kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai hedikwatar ‘yan sanda ta Lafenwa da ke Abeokuta.
Matar ta shaida wa ‘yan sanda cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ta aika ‘yarta tare da wanda ake zargin domin yin ado a wani coci da ke unguwar Ita Oshin na garin Abeokuta.
A cewarta, a lokacin da suka isa harabar cocin, sun hadu da wasu mata da suka zo share cocin a shirye-shiryen gudanar da ibadar ranar Lahadi.
Mahaifiyar ta ce “matan suna fita bayan sun share cocin, wanda ake zargin ya yi amfani da damar kasancewa shi kaɗai tare da wance yayi yimata fyaden a cikin cocin.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi a ranar Alhamis, ya shaida wa manema labarai a Abeokuta cewa, biyo bayan rahoton, DPO na Lafenwa, CSP Kayode Shadrach, ya yi karin bayani ga jami’an da suka gudanar da bincike domin bin diddigin wanda ake zargin.
Ya ce da sauri jami’an ‘yan sandan suka shiga wurin da lamarin ya faru kuma nan take suka kama wanda ake zargin wanda “tun daga nan ya amsa laifinsa.”
Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wanda ake zargin cikin gaggawa sashin yaki da fataucin bil’adama da cin zarafin yara na sashen binciken laifuka da leken asiri na jihar domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
A wani labari Kuma na daban.
Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ibrahim Matane, ya tabbatar da kisan wasu yara shida da wani jirgin yakin sojin Saman Kasar Nan NAF ya yi a jihar.
Matane ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin wanda ya faru a makon jiya, inda ya ce an kashe yaran ne a wani samame da aka kai wa ‘yan ta’addan.
Lamarin ya faru ne a unguwar Kurebe da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Da aka tambaye shi ko wani jirgin yakin NAF ya kashe yara 6?, Matane ya amsa da cewa, “Eh, hakan ya faru, gwamnati na duba lamarin kuma ana ci gaba da bincike don gano me ya faru.”
A cewar shugaban gamayyar kungiyoyin Shiroro, Salis Sambo, wanda ya zanta da wakilin Jaridar Daily Trust, ya ce yaran sun mutu ne a lokacin da jiragen yakin suka yi kokarin Saka bam ga wasu ‘yan ta’adda da suka shiga cikin al’umma domin tsira da rayukansu.
Ya ce yaran da abin ya shafa na dawowa ne daga rafi da suka je diban ruwa, inda ya ce hudu daga cikin yaran ‘yan gida daya ne.
“’Yan ta’addan ne suke kaiwa hari. A wancan makon an kai hare-hare ta sama kusan hudu a Shiroro kuma an kashe ‘yan ta’adda da dama. ‘Yan ta’addan sun shiga cikin al’umma domin samun mafaka inda aka harba bama-baman, lamarin ya shafi yaran. Ba da gangan ba ne, ”in ji shi.
Sambo ya ce wani mutum ya rasa ‘ya’yansa mata biyu da jikoki biyu a yayin lamarin.