Majalisar musulmi a Birtaniya ta zaɓi mace a matsayin shugaba a karon farko.
Zara Mohammed ta ce tana fatan zaɓenta a matsayin Sakatare Janar na Majalisar Musulmai ta Birtaniya zai zama ƙwarin guiwa ga mata da matasa su kai ga ga matsayi na shugabanci.
Masaniya dokokin kare hakkin dan adam ce. Za ta yi wa’adin shugabanci na shekara biyu.
An kafa majalisar ne a 1997 kuma ta ƙunshi masallatai 500 da makarantu da ƙungiyoyin musulmai.