Majalisar dokokin jihar Kano ta zabi Hon. Kabiru Hassan Dashi a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar dokokin ta jihar Kano.
Hon. Dashi ya kasance dan majalisa mai wakiltar al’ummar karamar hukumar Kiru dake jihar Kano.
Majalisar ta zabe shine yayin zamanta na yau Litinin, wanda ya gudana bisa jagorancin shugaban ta Hamisu Ibrahim Chidari.
Zaben nasa ya biyo bayan ajiye mukamin da tsohon mataimakin shugaban majalisar Hon. Zubairu Hamza Massu yayi wanda ya sauya sheka zuwa jam’iyar NNPP daga APC.
Kabiru Dashi, ya karbi rantsuwa a wajen daraktan shari’a na majalisar Nasidi Aliyu yayin zaman majalisar na yau.
Haka zalika yayin zaman shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya karanta takardar dan majalisar jiha mai wakiltar Bebeji Abubakar Uba Galadima, shima dake bayyana ficewar sa daga jam’iyar APC zuwa NNPP.