Daruruwan manyan mutane da dubban talakawa a yau Talata, sun yi cincirindo a filin wasan jarumai na kasa, dake Lusaka, babban birnin Zambia, domin halartar bikin rantsar da sabon Shugaban kasar, Hakainde Hichilema.
Mutane da yawa sanye da jajayen riguna da huluna, sun fara taruwa a filin wasan tun da misalin ƙarfe 4 na asuba.
Sun fara isowa da wuri ne, domin tabbatar da samun kujerun zama kafin lokacin da aka shirya fara bikin da ƙarfe 11 na safe.
A cikin jawabin da ya gabatar bayan an rantsar da shi, Hichilema ya ce, gwamnatinsa za ta yi kokari domin amfanin dukkan al’umar kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: An tumbuke Kakakin majalissar Jihar Kebbi
Ya ce, gwamnatin sa za ta gyara tattalin arziki, da bunkasa ta, domin fitar da mutane daga kangin talauci.
Ya Kara da cewa, gwamnatinsa za ta yi kokarin cika alkawuran da aka dauka yayin yakin neman zabe, kana gwamnatinsa za ta yi kokarin dawo da martabar doka da mutuncin mutanen kasar
Hichilema, wanda ya zama shugaban kasar Zambia na 7, ya kara da cewa, yaki da cin hanci da rashawa zai zama ginshikin gwamnatin sa.
A wani labarin Kuma na daban
Makarantar horas da Jami’an soji ta kasa ta tabbatar da kashe manyan jami’an ta biyu, Laftanar Cdr Wulah, da Flt Lt Cm Okoronwo, tare da garkuwa da Manjo Datong, a wani hari da yan bindiga suka kai makarantar a safiyar yau Talata.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar Manjo Bashir Muhd Jajira fitar a yau, ya ce, lamarin ya faru ne a cikin Afaka dake makaranta, da sanyin safiyar yau Talata.
Ya kara da cewa, Jami’an makarantar, tare da hadin gwuiwar jami’an Barikin 1 Division, da na rundunar horas da Jami’an sojin sama, da kuma sauran hukumomin tsaro, na kokarin farmakan yan bindigan.
Sanarwar ta ce “A safiyar yau wasu Yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, sun afka cikin makarantar horaswan na Afaka, inda suka kashe manyan jami’ai soji biyu, da kuma yin garkuwa da guda”
Kazalika sanarwar ta ce, ” Yankin Makarantar da kuma sabbin jami’an dake samun horo a Makarantar na cikin koshin lafiya. Inda kuma muke sanarwa da al’uma cewa, nan bada jima wa ba, za’a kama wadannan yan bindigan, sannan kuma za’a kubutar da jami’in da suka sace” inji sanarwar