Wani gungun ’ya’yan jam’iyyar APC na ƙoƙarin ganin an maido da dakataccen Shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole kan kujerarsa.
Babban daraktan Ƙungiyar Gwamnonin Masu yunƙurin Kawo ci gaba (PGF), Salihu Lukman Mohammed, ya bayyana haka a wasiƙarsa ga shugaba jam’iyyar na riƙo, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe.
Idan Oshiomhole ko wani daga Kudu ya zama shugaban jam’iyyar, to ɗan Arewa ne zai ƙara yin takarar shugabancin ƙasa a zaben 2023.
Mohammed ya yi zargi cewar, gungun mutanen jiran lokacin taron jam’iyyar na ƙasa suke yi, sun kuma gama shirya yadda Oshiomhole zai shiga takarar shugabancin jam’iyyar.
Ya kuma yi zargin za a juya ra’ayin waɗanda za a ba wa damar zaɓen domin Oshiomhole ya koma kujerarsa.
Mohammed ya nemi kwamitin Buni ya ɗauki mataki da wuri domin kauce wa matsalar da ka iya bijirowa a lokacin taron jam’iyyar.
“An yi duk ƙulle-ƙullen da za a yi na ganin Adams Oshiomhole ya shiga takarar zaɓen ya kuma dawo matsayinsa na Shugaban jam’iyyar APC, a babban taron jam’iyyar na ƙasa.
“Hakan ba matsala ba ne, sai dai matsi da tursasa shugabanin jam’iyya su ɗauki zaɓen kamar ya fi komai muhimmaci shi ne abun damuwa.
“Ya fito ƙarara cewar Kwamaret Oshiomhole da wani sashe na ƙusoshin jam’iyyar APC na neman nasarar zaɓen ko da ta haramtacciyar hanyar ce.
“Hatta kiran da Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi na a yi adalci a zaben Edo domin a ba mutane ‘yanci, ba zai hana su yin abun da suka yi niyya ba”, inji Mohammed.