Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana shirin kidayar jama’a na kasa a shekarar 2023 a matsayin “wanda ake bukata cikin gaggawa” ga gwamnatin tarayya da na kananan hukumomi domin tunkarar kalubalen da al’umma ke fuskanta, da matsalar rashin tsaro da ake fama da shi, tare da samar da kayayyakin aiki ga al’umma kasar nan. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Da yake jawabi a wajen taron wayar da kan masu ruwa da tsaki da hukumar kidaya ta kasa (NPC) ta gudanar a jihar Kaduna a ranar Litinin, Gwamna Nasir El-Rufai ya ba da misali da wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta yi na inganta kayayyakin more rayuwa a sassa daban-daban na jihar, inda ya ce, ya yi hakan ne, domin biyan bukatun al’umma a dukkan kananan hukumomi 23 dake Kaduna
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Za Mu Kara Wa’adin Dena Amsan Tsofaffin Kudi Ba—Emefiele
Ya ce, sauye-sauyen da za a yi a shekarar 2023 za su kara inganta aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi masu rauni da kuma tabbatar da cewa ba mu bar kowa a baya ba.
El-Rufai ya kara da cewa, ana bukatar kidayar jama’a cikin gaggawa domin ganin an aiwatar da manufar bunkasa kasar nan, don samar da ci gaba mai dorewa da sauran manufofin gwamnati, ya kara da cewa, kidayar 2023, idan an gudanar da shi da kyau, zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi al’umma. kasar .
Gwamnan, a madadin gwamnatin jihar Kaduna, ya bayyana kwarin gwiwar cewa, kidayar jama’a ta kasa, tana da himma da kuma karfin da za ta iya samar da kidayar “amintaccen, abin dogaro, karbuwa da nasara” ga Nijeriya.
Daga cikin dukkan matakan shirye-shiryen da aka sanya a gaba, El-Rufa’i ya ce, shiri ne na zuwa kidayar jama’a na shekarar 2023.
Elrufai ya kara da cewa, bayanan jama’a na da matukar muhimmanci ga tsare-tsare na ci gaba kuma duk wata gwamnati da ke da muradin samun ci gaba na bukatar bayanai na yau da kullum kamar yadda mutane nawa ke bukatar ababen more rayuwa kamar wutar lantarki, samar da ruwan sha, makarantu, gidaje, wuraren kiwon lafiya, ilimi da makamantansu.
An fara tabbatar da shirye-shiryen gudanar da kidayar jama’a a shekarar 2023 a watan Afrilun da ya gabata, bayan wani taron Majalisar kasar nan. Inda Aka tsara gudanar da shi tsakanin watan Maris da Afrilun shekarar 2023, ƙidayar za ta kasance ta farko a ƙasar nan tun bayan 2006.
A wani labarin kuma, Gobe Buhari Zai Kaddamar Da Sabbin Takardun Kudin Naira – Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya tabbatar da cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da takardar kudin Naira a gobe Laraba 23 ga watan Nuwamba, shekarar 2022.
Emefiele ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin kudi na babban bankin kasa na wata-wata a Abuja.