A kokarinsa na Samar da aiki ga matasan jihar Kaduna Sanata Malam Uba Sani Mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya ya cigaba da Ayyukan alkhari ga Al’ummarsa.
Idan dai ba a manta ba a ranar 2 ga watan Satumban na Shekarar 2021 data gabata ce, Sanata Uba Sani ya jagoranci wata babbar tawaga da ta kunshi manyan jami’an gwamnatin jihar Kaduna, da ‘yan jarida a wani rangadin aikin gina cibiyoyin wasanni daya ke bayar da gudunmuwa a matsayin wani yunkurin kafa shiyyar sa.
Tawagar da suka kai ziyarar akwai tsohon kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kaduna, Farfesa Kabir Mato, da kuma mai bai wa Gwamna El-Rufai shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa, Mista Olumuyiwa Adekeye.
Cigaban aikin gina cibiyoyin wasanni zai samar da damammaki da dama ga matasan mu, don bunkasa hazakarsu, da inganta zaman lafiya musamman a daidai lokacin da jihar ke cike da matasa masu hazaka a fannin wasanni daban-daban.
Sanatan ya yi imanin cewa wasanni na daya daga cikin manya-manyan abubawan da ka iya Samar da damar daukar ma’aikata. Idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata kuma aka bunƙasa fannin a matsayin kasuwanci.
Kazalika yayi nuni da cewa, yana da yuwuwar bayar da gudummawar gaske ga yaƙi da talauci da rashin aikin yi na matasa.
Wuraren da ake cigaba da Ayyukan a Halin yanzu sun ha’da da:
1) Cibiyar Wasanni Narayi, dake Makarantar Government day secondary school Narayi a karamar hukumar chikun.
2) Cibiyar Wasanni Kajuru, dake Makarantar Sakandaren Gwamnati Kajuru.
3) Cibiyar Wasanni Tudun Wada, dake Government Secondary School Kaduna South(GCK)
4) Cibiyar Wasanni Rigasa, Makarfi Road, Rigasa, karamar hukumar Igabi
5) Cibiyar wasanni Kawo, a Dallet girls sSecondary school kawo, na karamar hukumar Kaduna North.
Warren Wassanni da ake ginawan sun ha’da da;
1. Gym
2. (5 Aside) Wasan kwallon Kafa na yanwasa biyar.
3. Kwallon Raga
4. Kwallon Kwando
5. Filin wasa
6. 2 Traditional Wrestling, Wasannin Gargajiya irin su (Dambe & kokuwa)
7. Spectators stand, ( Wuraren Tsayuwar Yan Kallo)
8. Green area/pave ways
Rubutuwa Arc Abubakar Rabiu Abubakar, Fassara MIKIYA.
Editor: Uzairu Lawal Rigasa daga Jaridar Dimokuradiyya