Bayan tsagaita wuta na tsawon watanni biyar. Ana ci gaba da gwabza fada a yankin Amhara da ke arewacin kasar Habasha mai iyaka da Tigray.
Rahotanni sun nuna cewa sojoji sun karbe iko da Kobo na Amhara a ranar Asabar din da ta gabata, bayan sun kutsa zuwa kudu kusa da kan iyakar kasar.
BBC ta ruwiaito cewa, A baya dai rundunar sojin kasar ta ce za ta janye dakarunta daga garin ne domin gudun kada a samu asarar rayuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Wani Abu Zai Faru Nan Bada Dadewa, Inji Wike
Mazauna garuruwan da suka zanta da kafar yada labarai ta BBC sun ce ana ci gaba da gwabza fada a kan tsaunukan da ke yankin kuma lamarin ya yi kamari.
A halin da ake ciki hukumomi a Woldia da Dessie, manyan biranen Amhara guda biyu da ke kusa da yankin sun sanya dokar hana fitan dare.
A wani bangare kuma Gwamnonin yankunan kasar Habasha da suka hada da Oromia da kuma yankin Somali dake gabas sun bayyana goyon bayansu ga sojoji da kuma yankunan Amhara da Afar wadanda rikicin ya sake barkewa.
A daidai lokacin da ake gwabza yaki a shekarar data gabata bangarorin biyu sun aika da dakarun sj zuwa fagen dagan.
Haka kuma wasu bayanai da aka wallafa a kafafen sada zumunta sun nuna cewa kan iyakar yankin Tigrai da makwabciyarta Eritriya ana fargaban cewa yakin zai iya shafan yankunan.
Da yake jawabi babban jami’in yankin Tigrai Getachew Reda ya yi ikirarin cewa mambobin rundunar sojojin Habasha na gabashin kasar sun tsallaka kan iyaka domin hada kai da kawayen Eritrea.
Ana shi bangaren rahotanni sun nuna cewa, firaministan kasar Abiy Ahmed, bai yi wani jawabi ga yan kasar ba, tun bayan barkewar yakin, yayin da firaministan ke ziyarar aiki a kasar Aljeriya.
A WANI LABARIN KUMA: Da Dumi-Duminsa: Shekarau Ya Koma PDPA Hukumance, Bayan Wata Uku A NNPP
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP a hukumance.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Wannan dai na zuwa ne bayan watanni uku da komawar Shekarau daga jam’iyyar APC zuwa NNPP