Daga Usman Salisu Gurbin Mikiya
Bayan kisan ƴan Arewa 4 a yankin Orlu da wasu 3 a garin Amaka na jihar Imo, ƴan Arewa na ci gaba da zaman dar-dar a yankin, sakamakon hare hare da ƴan kungiyar Biafra ke kai musu.
Rahotan da jaridar Daily Trust ta samu ya bayyana yadda ƴan kungiyar ta Biafra ke ci gaba da kai hari ga masu sana’ar nama a garin Owerri Babban Birnin jihar.
Rahotanni sun shaida cewa ƴan kungiyar sun ziyarci masu sana’ar naman ne da nufin su saya daga baya suka ki biya, wanda hakan ya jawo hargitsin da suka yi amfani da damar wurin bindige masu sana’ar siyar da naman.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, shugaban Hausawa na garin Owerri Sani Ahmed Mai Rago, ya shaida cewa an yi jana’izar mamatan a ranar Jumu’a bayan dauko gawar mamatan
ya kara da cewa ya zuwa yanzu dai an kashe ƴan Arewa 11 a tsakanin makonni 2 a jihar
Ko wane Mataki Hukumomi zasu bi domin magance wannna gagarumar Matsalar