Ana cigaba da Zaman Ɗar-Ɗar, yayin da Babbar Kotu zata yanke hukunci kan Canje Sheƙar Ayade
Zaman ɗar-ɗar na cigaba da haihuwa a ɓangaren Gwamna Ayade na Jahar Cross River, a yayinda Babban Kotun Abuja, zata yanke hukunci akan ƙarar da aka shigar kan canja Sheƙar Gwamnan.
Ana saran Mai Shari’a Taiwo Taiwo zai yanke hukunci akan tabbacin fita Jam’iyyar ko akasin haka akan canja Sheƙa na Gwamna daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnan Zamfara Matawalle ya raba Motoci 260 ga Sarakunan Gargajiya
Ya zuwa lokacin haɗa rahoton, ɗaruruwa magoya baya da masu jaje ga Gwamnan, sun cika Farfajiyar Kotun, suna cigaba da musu akan yanda hukuncin zai kasance.
Duk da jiya ya kamata a yanke hukuncin a jiya, an canja zuwa yau, biyo bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara.
Mai Shari’a Taiwo ya dage hukuncin domin bashi damar duba hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara akan abinda ya shafi canja Sheƙar.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Enugu ta bayyana cewar, wannan canja Jam’iyyar babu laifi a cikin shi, yama taɓa hukuncin Ƙungiya kamar yadda yake a sashe na 40 na Kundin Tsarin Mulkin 1999.
Ben Ayade da Mataimakin sa sun canja sheƙa daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC, Wanda ya Sanya PDP tayi kira ga Kotu data ayyana kujerar ba kowa.
Haka zalika, Mai Shari’a Taiwo ana jiran shi a yayinda yake a ɗakin Kotu domin yanke hukuncin.