Kwamishinan Shari’a na Jihar Legas, Mista Moyosore Onigbanjo ya ce ana cin zarafin daya daga cikin ‘yan mata hudu a jihar kafin ta cika shekara 18.
Onigbanjo, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Amsa Rikicin Cikin Gida da Cin zarafi ta jihar Legas (DSVRT), ya fadi hakan ne a Ikeja a ranar Laraba a yayin wani taron manema labarai na tunawa da watan Satumba a matsayin watan Fadakarwa kan rikicin cikin gida da kuma cin zarafi.
Ya ce a binciken da gwamantin jihar Legas ta yi tare da hadin guiwar UNICEF, ya tabbatar da cewa a cikin ‘yan mata hudu sai ka samu mace daya da aka ci zarafinta kafin ta kai shekara 18 a duniya.
Kazalika ya ce a cikin maza ma ana samun namiji daya cikin goma da ake cin zarafinsu kafin su kai ga shekara 18.
Ya nemi da a rika bai wa yara kulawa ta musamman domin kange su daga fadawa hannun wadanda za su rika cin zarafinsu, wanda ya ce wanann na daya daga cikin abin da ka iya dakile cin zarafin masu kananan shekaru.