Ana fargabar jami’an tsaro sun mutu yayin da wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis da yamma suka harbe ‘yan sanda da jami’an kwastam da ke bakin aiki a wurare daban-daban a jihar Enugu.
An ruwaito cewa yan ta’addan dauke da makamai sun kai hari a shingen binciken kwastam dake cikin garin Ozalla dake kan hanyar Enugu zuwa Port Harcourt, kusa da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Najeriya (UNTH), Iituku-Ozalla da misalin karfe 1:30 na rana.
A cewar wani shaidar gani da ido, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an kwastam din da ba a san ko su wanene ba, inda nan take mutum daya ya mutu tare da jikkata wasu uku.
Shaidar gani da ido ya ce, “Na ga daya daga cikin jami’an kwastam ba ya motsi; yayin da wasu uku suka ji Rauni sosai inda Kuma wasu yan kasa nagari suka taimaka musu zuwa asibitin UNTH da ke kusa.”
Kazalika An kuma ruwaito cewa, a yayin da lamarin ya faru a unguwar Lomalinda da ke kan titin Ugwuaji, ‘yan bindigar sun harbe ‘yan sandan da ke bakin aikinsu, lamarin da ya sa ake fargabar mutuwar su nan take, yayin da wasu kimanin hudu suka samu munanan raunuka.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin wanda ya faru da misalin karfe 2 na rana, ya bar titin Ugwuaji babu kowa har da ababen hawa har na tsawon sa’o’i biyu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ndukwe ya ce: “A halin da ake ciki, an fara farautar ‘yan bindigar. Za a sanar da ƙarin bayani Nan gaba kadan.
Comments 1