Ana zargin wani hafsan soja mai mukamin Manjo ya kashe kansa a Jihar Kaduna.
Manjo UJ Undianyede, wanda tsohon kwamanda ne da ya jagoranci yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, ana zargin ya kashe kansa ne kafin wata kotun soji da aka gurfanar da shi a gabanta ta yanke mishi hukunci.
Majiyoyin na sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa, Manjo UJ Undianyede ne ya harbe kansa ne kimanin sa’a 72 kafin kotun sojin ta yanke mishi hukunci kan zargin aikata wasu laiufuka a lokacin da yake kwamandan yaki da ta’addanci.
Majiyoyin sun ce ya harbe kansa ne ta hanyar amfani da karamar bindigarsa a harabar jami’ar sojoji ta NDA da ke Kaduna a ranar Litinin.
Daya Daga Cikin majiyoyin na rundunar soji ya bayyana cewa lamarin yafaru ne a ranar Laraba da dare,
Kana ya ce A lokacin da yake jagorantar yakin, ana zargin shi da wasu abokan aikinsa da aikata wasu laiufuda da a kansu aka gurfanar da su a Babbar kotun Rundunar Soji ta 1 da ke Kaduna.
Rayhaan Rediyo ta ruwaito cewa ana zargin mamacin ne da aikata almundahana da watsi da aiki, tsaurin ido, sakaci da aiki, da dai sauransu.
Wata majiyar kuma ta alakanta rasuwar da tsananin damuwar da Manjon yake ciki, saboda ya dade a fagen yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
Manjo Manjo UJ Undianyede yana daga cikin rukuni na 55 da aka yaye daga makarantar horas da dakarun soji ta NDA, kuma a watan Satumba ake sa ran yi musu karin girma zuwa mukamin Laftanar-Kanar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ko da aka tuntubi kakakin Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, kan lamarin, ya ce bai samu labari ba.
Amma da ta ce, da aka tuntubi mai magana da yawon kwalejin NDA, Manjo Bashir Jajira, ya karyata labarin, yana mai cewa babu wani hafsan soji da ya kashe kansa.
Shi kuma Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Rundunar Soji ta 1 da ke Kaduna, Manjo Musa Yahaya da aka tuntube shi, ya ce ba shi da masaniyar wata kotun soji da ke zama a rundunar.
Comments 1