By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadin da ta gabata ne mazauna garin Gashu’a, hedikwatar karamar hukumar Bade ta jihar Yobe, aka jefa su cikin bala’i, sakamakon wata babbar fashewa da ta afku a garin.
Gashu’a na da tazarar kilomita 188 daga arewa da Damaturu, babban birnin jihar Yobe kuma mahaifar shugaban majalisar dattawa mai ci, Ahmad Lawan ne.
Fada Akan Budurwa Yayi Sanadiyyar Mutuwar Samari 3 A Jihar Kwara
Lamarin ya faru ne a wani gidan giya da ke unguwar Abasha a cikin garin a lokacin da musulmi suke sallar magariba.
Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta shaida wa wakilinmu cewa, “muna gudanar da sallar magariba ne da karfe 8 na dare, kwatsam sai muka ji karar fashewar wani abu mai karfi, bayan an kammala sallar, sai aka ce mana wasu bama-bamai ne suka tashi a unguwar Abasha.
Duk da cewa bayanan fashewar jaridar DAILY POST ta tattaro cewa mutum daya ya mutu, yayin da wasu bakwai suka samu raunuka daban-daban kuma an kai su Asibitin kwararru na Gashu’a domin kula da lafiyarsu.
Har ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wata kungiya da ta dauki alhakin fashewar bam, amma da dama sun yi imanin cewa lamarin ya yi kama da wanda ‘ya’yan kungiyar Boko Haram mai tsatsauran ra’ayi suka yi a wasu sassan yankin Arewa maso Gabas.
Lamarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan da mayakan Boko Haram suka kutsa cikin garin Geidam cikin dare, inda suka kashe mutane kusan goma sha daya.
Har ila yau, a cikin mako guda, wasu bama-bamai biyu sun tashi a wasu sassa na Jalingo na jihar Taraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
An bayar da rahoton cewa, ‘yan ta’addar ISWAP sun dauki alhakin tashin bama-bamai na birnin Jalingo.
Comments 1