Masu kamuwa da annobar cutar korona na ci gaba da raguwa a Nijeriya, a inda hukumar dake daƙile cututtuka masu yaɗuwa a kasar NCDC ta ce a ranar Juma’a an samu ƙarin mutum 66 da suka kamu da cutar, sannan an sallami mutum 127 bayan sun warke daga cutar.
Bisa sabbin alkaluman hukumar, Inugu ce ke kan gaba da yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar da mutum 18.
A yayin da mutum 10 kacal suka kamu da cutar a Kaduna, sai kuma jihar Legas ta zo ta uku inda mutum 17 suka kamu da cutar.