Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Ana sa ran yawan al’ummar duniya ya kai biliyan 8 a ranar 15 ga watan Nuwamban wannan shekarar, kamar yadda hasashen da majalisar dinkin duniya ta yi a wannan Litinin din ya nuna.
Hasashen ya nuna cewa Indiya za ta zarce China a yawan Jama’a a cikin shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/an-matsawa-gwamnatin-afrika-ta-kudu-kan-binciken-wadanda-suka-kai-hari/
Sakataren majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya ce wannan ci gaba da aka samu a bangaren yawan jama’a, tuni ne a kan hakkin da ya rataya a kan al’ummar duniya wajen kula da muhali da yanayi, sannan kuma lokaci ne na nazari a kan inda aka gaza wajen kulawa da juna.
Hasashen da hukumar kulada tattalin arziki da zamantakewa ta majalisar dinkin duniya ta yi ya nuna cewa a karon farko tun bayan shekarar alif dari tara da hamsin 1950 yawan al’ummar duniya ba ya karuwa cikin sauri.
Rahoton hasashen ya ce yawan al’ummar duniya na iya kai wa biliyan 8 da rabi a shekarar 2030, da biliyan 9 da miliyan dari 7 a 2050, inda daga nan zai tsaya a inda yake har zuwa karni na 22.
A yayin da kasashe masu tasowa da dama ke bin tsarin takaita haihuwa, fiye da rabin karuwar yawan al’umma zai kasance ne a kasashe maso tasowa 8, wato, Jamhuriyar dimokaradiyya Congo, Masar, Habasha, Indiya, Najeriya, Pakistan, Philippines da kuma Tanzania