Hukumar kare hakkin mai siye da siyarwa ta jihar Kano ta zargi hukumar Yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da yunkurin bata mata suna a idon jama’a.
Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Musbahu Aminu Yakasai ya fitar a Juma’ar da ta gabata.
A cewarsa babu kanshin gaskiya a ikiranin da hukumar ta Anti-currption ta yi cewa ta gayyaci shugaban hukumar Idris Bello Dambazau amma yaki zuwa.
A cewarsa wadannan hukumomi duk suna karkashin kulawar gwamanatin Kano, maimakon a mika korafi ga gwamnanti sai aka fita waje ana bata mata suna.
Wanda kuma a cewarsa hakan bai kamata, domin dukkan hukumomin biyu suna aikin alumma ne.
Latsa wannan muryar ta kasa domin jin karin hasken da yayi yayin ganawarsa da Jaridar Dimokuradiyya.