Kungiyar Cinikayya ta Duniya, WTO, ta kira taro na musamman a wannan Litinin domin zaben shugabar kungiyar da ake kyautata zaton Tsohuwar Ministar Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ce za a nada a wurin wannan zama.
Tun a watan Nuwamba aka yi tsammanin yin ittifakin bai wa Ngozi Okonjo-Iweala wannan kujera amma Tsohon Shugaban Amirka Donald Trump ya yi ta nuna turjiya kan yunkurin. Sai dai goyon bayan da a yanzu gwamnatin Amirka ta Joe Biden ta ba ‘yar Najeriyar ya sanya jama’a gamsuwa cewa ita ce za a zaba a zaman na yau a matsayin ‘yar Afirka kuma mace ta farko da za ta jagoranci WTO din. Ana sa ran Ngozi Okonjo-Iweala ta yi jawabi jim kadan bayan an sanar da zaben nata a wannan matsayi mai muhimmanci.