Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki SERAP, ta nemi a gaggauta dawo da naira biliyan 1.14 da aka baiwa jamhuriyar Nijar domin sayen motocin hukuma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.
SERAP a shafinta na Twitter da aka tabbatar a ranar Laraba ta yi wannan bukatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kuna zuwa Abuja Kuka Kan Zaben Abia, Ku Sani Abuja Daban Abia Daban – Abdullahi Adamu
Ministar kudi Zainab Ahmed ta tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 1.14 don samar da motoci kirar Toyota Land Cruiser V8 guda 10 ga Jamhuriyar Nijar.
Ministar ta yi ikirarin cewa a kodayaushe Najeriya na bayar da irin wadannan ayyukan ga kasashe makwabta da suka hada da Chadi, Kamaru, da sauran su.
Ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da ‘yancin yanke shawara domin amfanin kasar.
A cewarta, “Najeriya ta zama dole ta tallafa wa makwabtanta, musamman ma na kusa, domin inganta karfinsu na tabbatar da tsaron kasashensu.”
“Wannan dai ba shi ne karon farko da Najeriya ke taimakawa Jamhuriyar Nijar, Kamaru ko Chadi ba.”
Sai dai ‘yan Najeriya ba su amince da yadda aka raba kudaden ba a daidai lokacin da kasar ke fama da rikice-rikice kamar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) take yi na kusan watanni shida da kuma wasu kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta wadanda ke bukatar a dauki matakin gaggawa.
SERAP ta wallafa a shafinta na Tuwita cewa, “Dole ne gwamnatin Buhari ta gaggauta neman hukumomin Jamhuriyar Nijar da su dawo musu da Naira biliyan 1.14 da aka amince musu na sayen motoci, sannan su yi amfani da kudin wajen rage kudaden da ake bawa ASUU, don haka yaran talakawa su koma makaranta”.