A yau Alhamis 13 ga watan Fabarairun 2020 tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya, Janar Murtala Ramat Mohammed ke cika shekara 44 da rasuwa.
A wancan lokacin wasu sojoji ne da suka yi yunkurin juyin mulki suka kashe shi a rana irin ta yau a shekarar 1976 a Legas.
Ya rasa ransa ta hanyar harbi a daidai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wurin aiki a wannan rana.
Murtala Mohammed shi ne mutum na hudu da ya zama shugaban Nijeriya tun bayan samun ‘yancin kanta a 1960 daga turawan mulkin mallakar Birtaniya.