A Nijeriya, yayin da dakarun kasar ke ci gaba da aikin kakkabe ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya a Yankin Arewa maso Yammacin kasar, wasu masu sanya ido na zargin cewar, ana samun zagon kasa a aikin daga bangaren jami’an tsaron da kuma hukumomin kula da sadarwa, abin da ya sa ‘Yan bingigar ke ci gaba da kai hare hare.
Wannan ya biyo bayan kashe kashen da aka samu a wasu Yankunan Jihar Zamfara da Neja.
Injiniya Kelani na daya daga cikin masanan da suke ganin ana yi wa jami’an sojin zagon kasa a yakin da suke yi da ‘yan bindigar.