Rahotannin dake shigo mana ta hanyar majiyarmu, ta labarto cewa ana zargin Farfesa MT Ladan da satar fasahar rubutu, lamarin da ya sanya ake zaton zai ajiye aikinsa a Jami’ar domin gujewa abin kunya na hukunta shi.
Majiyarmu ta Jaridar Madubi ta labarto cewa; a wani mataki na kaucewa fadawa jin kunya da kuma fuskantar hukunci daga mahukumta Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, Farfesa Muhammad Taufeeq Ladan, Babban Daraktan makarantar fadada karatun Shari’a ta Nijeriya, NIALS na neman ajiye aikinsa da yake yi da jami’ar ABU sakamakon zarginsa da satar fasahar rubutu, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar mana.