A yau ne Rahotanni daga kasar Nijar suka bayyana cewa; an kama ‘yar jarida Samira Sabou, lamarin wanda ya tashi hankulan ‘yan Jaridu na Kasar Nijar dama Nijeriya, inda dalilan kama ta bai bayyana ba.
Wata majiya ta bayyana cewar Abba Mahamadou Issoufou dan gidan Shugaban kasar Nijar yana da alaka da fitaccen dan kasuwar makamai wato Boube Style féroce, wanda Samira ta gano hakan ta kuma bayyanawa duniya.
Samira ta kasance ‘yar jarida ce ga gwamnatin kasar ta Nijar, sai dai a kwanakin baya an tsigeta sakamakon kwaikwayon irin tsayuwar da shugaban kasar yake yi, wanda hakan ya jawo ta zama ‘yar jarida mai zaman kanta.
An bayyana Samira Sabou a matsayin tsayayyiyar ‘yar jarida da take zakulo labarin da zafi-zafinsu tare da yadawa a kasar Nijar kafin cafketa da gwamnatin kasar ta yi.