By Abbas Yakubu Yaura
An samu rudani a unguwar Kidenda dake karkashin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna inda aka ce sojoji sun harbe wasu ’yan uwa mata guda biyu har lahira a kasuwar.
Shedun gani da ido sun ce sojojin na tafiya cikin kasuwanni sai suka hangi wasu bakin mutane zaune akan babura suna kalubalantarsu.
Mazauna kauyen sun tashi tsaye lokacin da suka fara jin karar harbe-harbe da ake zargin sojoji na yi wa mutanen. A rikicin da ya biyo baya, ‘yan uwa mata biyu masu suna Nurayn mai shekaru 16 da Khadija ‘yar shekara 11, sun fuskanci harsashin bindiga a yayin da su ma suka yi kokarin guduwa daga wurin.
Kaninsu mai suna Salisu Shuaibu Kidanda ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa harbin harsashin da sojoji suka yi a wajen taron sun kashe su.
“Ko da su (sojoji) suka nufi Fulanin da suka gani a kasuwa, me zai sa za su harbe jama’a? ’Yan uwana mata na kokarin komawa gida domin kasuwa tana can bayan kauyen sai harsashi ya same su.
‘Yayin da muke magana sojoji ba su ma ziyarci iyayenmu ba don jajanta mana kan wannan aika-aikar da suka yi, ‘yan sanda ne kawai suka yi. Muna bukatar adalci domin ba za ku iya kashe ‘yan mata da ba su ji ba ba su gani ba haka nan kuma su bar su,” inji shi.
Wani mazaunin garin kuma ya ce bai kamata sojoji su yi harbi a kasuwa ba saboda Fulanin da suke shirin kai wa farmaki sun tsere cikin daji.
Daily Trust tace ta samu hotunan wadanda abin ya shafa kafin a yi musu sallar jana’izarsu a kauyen.
Da aka tuntubi mataimakin darakta, jami’in hulda da jama’a na rundunar soji ta daya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce an dauke shi zuwa Abuja inda aka canza masa wurin aiki, kuma ya umurci wakilinmu da ya tuntubi wani Laftanar Shehu wanda har ya zuwa lokacin hada rahoton bai samu jin ta bakin sa ba.