Wani bincike ya nuna cewa sojojin Birtaniya na musamman da ake kira SAS Sun kashe tare da tsare wasu mutane ba bisa ka idaba.
Wani sabon rahoto da aka fitar kan jami’an sojin, ya nuna sashe daya na rundunar sojin sun kashe a kalla mutum 54 a cikin wata daya zuwa shidda.
Kafar yada labarai ta BBC ta samu wasu bayanai da suka tabbatar da cewa shugaban sojojin ya kasa tsallake zargi kisan gillar da a keyi masa.
To sai dai ma’aikatar tsaron kasar tace sojojin Birtaniya sun gudanar da ayyukan su bisa kwarewa a kasar Afghanistan.
BBC, ta bayyana cewa, anyi wa Tsohon Shugaban runduna ta musamman Janar Mark Carleton Smith bayani akan zargin kisan gillar, to sai dai ba a kaiwa jami’yan yan sanda sakamakon bincike ba.
Janar Carleton-Smith, wanda ya jagoranci rundunar soji, kafin ya sauka a watan da ya gabata, ya ki cewa komai kan lamarin. Sashen bincike na BBC Panorama ta bincika ɗaruruwan shafuka na asusun SAS na aiki, gami da rahotannin da ke ɗauke da sama da gamman kashe kashe da suka gudana ba bisa kaida ba, waɗan da da ƙungiyar SAS ta kai a yankin Helmand a cikin shekara 2010 zuwa 2011.
Wasu da ake zargi da aikata laifukan yaki tare da tawagar rundunar ta musamman, SAS sun shaida wa BBC cewa suna sane da yadda jami’an SAS ske kashe mutanen da ba su dauke da makami a cikin dare.
Har ila yau, sun ce sun ga yan da ‘yan sandan sukayi a amfani da makamai da suka hada da bindigar kirar – AK-47 da wasu makaima i da aka dasa a wani wuri domin tabbatar da kashe wasu da ba su da makami.
Wasu da dama da suka yi aiki tare da sojoji na musamman sun ce, jamiyan SAS na fafatawa da juna donyin kashe-kashen masu yawa, kuma tawagar BBC ta binciki lamarin na kokarin samun adadi karin shaidu akan lamarin.
Sai dai, sakwannin imel na cikin gida, sun nuna cewa, manyan jami’an soji na musamman, suna sane da cewa, akwai damuwa kan yiwuwar kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, amma sun kasa kai rahoton zargin ga ‘yan sandan soji duk da wajibi ne yin hakan bisa tsarin doka.
Ma’aikatar tsaron kasar ta ce ba za ta iya yin tsokaci kan takamaiman zarge-zargen ba, amma bai kamata a dauki kin yin sharhi a matsayin amincewa da gaskiyar zargin ba.
Duk da haka, a binciken da ta yi na baya-bayan nan, BBC ta yi nazari kan sabbin rahotannin aiki da aka samu da ke bayyana asusun SAS na hare-haren dare. Mun samu wani rahoto mai kama da kama da cewa an harbe mutanen Afganistan saboda sun ciro bindigogin AK-47 ko gurneti daga bayan labule ko wasu kayan daki bayan an tsare su.