Wani matashi mai suna Musa David dan shekara ashirin da biyar a duniya a Sashen koyan harkokin kudi da aikin Banki da a Waziri Umaru Federal Polytechnic (WUFP) Birnin Kebbi ya kashe kansa. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
David ya kashe kansa ne a hannun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC a Birnin Kebbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa: Sama Da Mutane 300 Ne Suka Mutu A 2022— NEMA
Sai dai hukumar NSCDC ta musanta wannan zargi, wanda ya yi ta yawo a tsakanin Al’ummar babban birnin jihar a jiya Talata.
Kakakin NSCDC, Akeem Adeyemi, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ya ce, wannan rashin da’a da David ya yi ne ya tilasta wa Antinsa, Mrs Augustina Galadima, wacce ke zaune a gidan kwanan dalibai na Gangare, da ke Badariya, cikin birnin Birnin Kebbi, ta nemi taimakon wani jami’in NSCDC, wanda ake zargin ya kai shi ofishin hukumar gawarwaki domin tseratar da ransa
Ya gargadi jama’a game da illolin yada jita-jita tare da shawarce su da su rika tantance al’amura kafin su yada wa wasu.
DAILY POST ta ruwaito cewa kafin ya aiwatar da wannan aika-aika, ana zargin marigayi Musa da shan wasu abubuwa, wadanda ake zargin miyagun kwayoyi ne.
Tuni dai aka mika gawarsa ga ‘yan uwansa domin yi musu jana’iza.
A WANI LABARIN KUMA: Kotun Koli Ta Yi Watsi Da Hukuncin Da Ya Halasta Dan Takarar Gwamnan Ebonyi
Kotun koli ta yi watsi da hukuncin da aka yanke kan wanene halastaccen dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ebonyi a babbab zaben 2023 da ke tafe.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin mai shari’a Amina Augie, ta sanar a ranar Larabar nan cewa za a yanke hukuncin da karfe 3 na yammacin yau bayan sauraren gabatar da karar da lauyoyi suka gabatar ga bangarorin da ke cikin karar mai lamba: SC/CV/ 939/2022 da Ifeanyi Chukwuma Odii ya shigar.