Wani Uba Mai Shekaru 38 ya shiga hannun ƴan sanda sakamakon zargin sa da ake yi da yiwa wata ƴar shekaru 14 ciki a Yenagoa, Babban Birnin Jahar.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Bil’adama mai suna GRIT ƙarƙashin jagorancin Dise Ogbise ya bayyana haka ga ƴan sanda, wanda ya bada nasarar kama shi, ɗan asalin Ogani Wily Kaira, A Ogoni ta Jahar Rivers.
KARANTA WANNAN LABARIN: Damfarar Dala $24: Akwai yiwuwar Hushpuppi a ɗaureshi shekaru 20 gidan yari
Ogbise ya bayyana cewar GRIT ta samu labarin daga maƙwabcin sa, wanda ya bayyana cewar, yanzu haka tana da ciki na tsawon watanni 5, kuma mahaifin ta ne yayi mata.
Uban dai ya kasance yana cin zarafin ɗiyar tashi tun tana da shekaru 7, ta hanyar sanya mata hannu a gaban ta, amma lamarin ya ƙara taɓarɓarwa bayan mahaifiyar ta, ta rasu shekaru kaɗan.
A cewar Jaridar Nigerian Tribune, Uban da ake zargi ya mayar da ɗiyar tashi a matsayin mata a gadon auran su, a yayinda ƙaramar yarinyar mai shekaru 14 dake a karamar makarantar sakandare aji 3, tana kwanciya da uban nata, inda ƙannen ta ke kwantawa akan ƙasa.
Amma wani jami’in ɗan sanda ya shaida cewa a ofishin su na Ekeki, inda aka kai rahoton lamarin, sun kaɗu a yayinda yarinyar mai shekaru 14 ta bayyana cewa tana soyayya da ubanta.