Za a iya cewa ana zaton wuta a maƙera sai ga wutar ta tashi a masaƙa a sana’antar shirya fina-finai ta Bollywood dake ƙasar India, domin kuwa mafi yawan mutane na ganin cewar jarumin da ake zargin an kasheshi wato Sushant Singh Rajput ana maganar damuwa ce tayimasa yawa wanda ake ganin mafi yawan abin da yake kawo ciwon damuwa rashin gata ne wato muganen da gidansu bamasu hannu da shuni bane ciwon damuwa yafi kamasu.
Ana tsaka da zargin ko ciwon damuwa ne ya kashe Sushant Singh Fajput sai wasu labarai suka fito da zafi-zafinsu na wasu jarumai maza da mata suma da irin wannan ciwon damuwar yake damunsu kokuma ace sunyi irin wannan ciwon damuwar amma sun warke.
Ga jerin sunayen ‘ya’yan jarumai da kuma ‘ya’yan wasu manyan jarumai a masana’antar ta Bollywood:
1. Jaruma Sharada Kapoor tana daga cikin wadda irin wannan damuwa ta sameta wadda ta bayyana cewar lokacin da shahararren fim ɗinsu wato Ashiqui ya fito kuma da yadda fim ɗin ya samu karbuwa a idon diniya bayan fitowar fim ɗin tayi fama da irin wannan damuwar.
2. Jarumi Tiger Shruff wanda yake ɗa ne a wajen jarumi Jackie Shruff ya bayyana cewar lokacin da fim ɗin sa maisuna Flying Jett ya fita shima irin wannan damuwar ta sameshi.
3. Alia Bhatt itama mahaifinta maiba da umarni ne ta bayyana cewar itama ciwon damuwar ya sameta a shekarun baya wanda har tunaninta yaso ya taɓu wanda hakanan kawai sai taji kamar zata fashe da kuka batare da daliliba.
4. Itama Ira Khan ‘yar gidan shahararren jaruminnan wato Aamir Khan itama tayi fama da irin wannan ciwon damuwa har na tsawon shekaru kusan 5 da suka wuce, amma ita kanta ta bayyana cewar batafi shekara ɗaya da warkewa ba, har takeyiwa kanta da kanta tambayar cewar wai kodai bata da komai ne harda wannan cutar ta kamata?.
5. Varun Dhawan ɗan gidan maiba da umarni wato David Dhawan inda shima bayan fitar fim ɗin sa mai suna Badalpur irin wannan ciwon damuwar ya kamashi kuma ya shiga tsanani sosai.
6. Shuhana Khan ‘yar gidan shahararren jaruminnan wanda ya gigita masana’antar Bollywood da fina-finan soyayya wato Shahrukhan taɓa afkawa irin cikin wannan damuwar wanda har saka labarin tayi a shafinta na Imstagram wanda har ake ganin ko irin gayamata maganar da akeyi ce ta Kalmar mummuna inda akecewa fatarta bata da kyau shine ya dalilin shiga damuwar tata.
7. Shaseen Bhatt ‘yar uwa ga jaruma Alia Bhatt itama ta shiga tsnanin damuwa sosai lokacin da ciwon ya kamata.
Kusan dukkanin waɗanda aka lissafa ‘ya’yan manyan jarumai ne da kuma ‘ya’yan manyan masu bayar da umarni wanda dukkaninsu irin wannan cutar ta kamasu sannan kuma dukkaninsu suna da gata, amma kuma sai ga wasu suna tunanin cewar shima rasuwar Sushant Singh Rajput ciwon damuwa ne ya kawomasa ita bayan ana ta zargin kasheshi a kayi.