Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP), Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ana zubar da jini a Najeriya.
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da mataimakinsa dan takarar shugaban kasa, Bishop Isaac Idahosa a Abuja, Kwankwaso ya ce, ana jibar da jini a kasar nan, saboda munanan raunuka da suka yi mata yawa sakamakon rashin iya aiki da rashin gaskiya na masu gudanar da mulki.
Ya yi shagube kan gwamanatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Ya ce, “Gaskiyar magana ita ce, kasarmu tana zubar da jini daga wasu munanan raunuka da aka yi mata ko dai sakamakon rashin iya aiki ko rashin gaskiya na ma’aikatan gwamnati ko kuma rashin fahimtar yadda ake gudanar da al’adu daban-daban a kasa mai yawan addinai da kabilu daban-daban kamar namu.
“Rashin gaskiya da rashin hakurin su ya jawo munanan raunuka ga zamantakewar Najeriya. Tsananin son zuciya da salon tafiyar da mulkinsu ya jawo wa kasar nan munanan raunuka. Rashin sanin yakamata da rashin tausayinsu ya yi mummunar illa ga ruhin duk ‘yan Najeriya.
“Girman kai da kuma fahimtar hakkin su ya kara fadada laifin da ba daidai ba a kasarmu da kuma halin da ba a sani ba na shugabanci yana haifar da hadarin rashin tsaro.”
Kwankwaso wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne, tsohon ministan tsaro kuma tsohon dan majalisar dattawa, ya kuma koka kan hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi a kasar, yana mai cewa ba za a amince dahalin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu ba.
Ya kuma yi Allah wadai da rugujewar manyan makarantun kasar nan, inda ya yi alkawarin bai wa ilimi fifiko idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023.
Bishop Idahosa, yayin da yake karbar nadin nasa a matsayin abokin takarar Kwankwaso, ya ce Najeriya na cikin tsaka mai wuya, wani sabon salo na nan tafe.
“Najeriya ta cancanci sabon shirin gudanar da mulki da sabbin dabaru. Najeriya ta cancanci sabuwar yarjejeniya da za ta kawar da kasar daga rarrabuwar kawuna da kiyayya. Sabuwar yarjejeniyar da za ta kawar da kasar daga gazawa da rashin sanin yakamata; sabuwar yarjejeniyar da za ta kawar da kasar nan daga matsalar rashin tsaro da tattalin arziki,” inji shi.
Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi rajista tare da samun katin zabe domin samun damar kawo sauyi da ake bukata a kasar.
Bishop mai shekaru 57 wanda ya fito daga jihar Edo an bayyana shi a matsayin mataimakin dan takarar na NNPP a ranar Alhamis din da ta gabata.
Idahosa, kwararren injiniyan ne daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna, ya kuma yi digirin digirgir a fannin ilimin tauhidi, kuma ya auri Christiana Idahosa, kuma ya nada ’yara biyu.
Shi ne shugaban Bishop kuma babban Fasto na cocin the God First Ministry, dake Lekki a jihar , Legas.