By Ishaq Dabai
Wata dalibar jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Awka ta jihar Anambra, mai suna Precious ta mutu a yau Alhamis sakamakon fashewar tukunyar gas.
Rahotanni su bayyana cewa lamarin ya faru ne a daya daga cikin masaukin dalibai na jami’ar Ifite, Awka.Wasu rahotanni sun ce wasu daga cikin mazauna masaukin sun samu raunuka daban daban daga gobarar.
Wata majiya tace, “Budurwar ta makale a jikin bangon ginin daya rushe sakamakon fashewar tukunyar gas din kuma ta kone ta inda baza’a iya ganeta ba, Mafi yawan ɗaliban UNIZIK ne ke zaune a harabar.”
Kazalika wata majiyar kuma ta kara da cewa Obinna Anyanwu, ta bayyana fashewar ta faru ne a daya daga cikin dakin mutanen dake cikin ginin yayin da take dafa abinci da gas a cikin dakinta.
Sannan tace, “Daya daga cikin wadanda ke cikin gidan yana soya popcorn a cikin dakin lokacin da lamarin ya faru. Galibin dakuna a masaukin daliban abin ya shafa kuma an lalata kadarori da dama.
“A gaskiya mun yi kokarin kashe wutar amma ba mu iya ba har sai da jami’an hukumar kashe gobara suka iso. Mun kuma yi kokarin kubutar da yarinyar da bango ya rufta amma ba mu iya ba har sai ta mutu. ”