By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 5503 aka kama a jihar Anambra bisa zargin su da aikata laifukan kiyaye hadurra a tsakanin watan Mayu zuwa Nuwamba, 2021.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar, Mista Adeoye Irelewuyi,shine wanda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Awka, inda ya bayyana cewa wadanda suka aikata laifukan sun kai mutane 6687 da suka hada da keta alfarmar sanya madaurin jiki yayin tuki amma uku ne kawai aka gurfanar dasu a gaban kotu a tsawon wannan lokacin.
A cewar Irelewuyi, wanda ya karbi ragamar hukumar a cikin watan Mayu, yace rundunar kiyaye hadura ta jihar Anambra ta kuma tattara bayanan hadarurruka 110 wanda 27 daga cikin su suka yi sanadiyar rasa rayuka.
Sannan ya kuma yi sanadiyar mutuwar mutane 37 tare da jikkata wasu 239 a cikin watanni bakwai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A yayin bukukuwan Kirsimeti dana sabuwar shekara, Kwamandan sashin ya sanar da cewa, rundunar ta gano wasu ‘yan ta’adda guda tara a jihar Anambra inda ake sa ran yawan zirga-zirgar ababen hawa zata karu, inda ya kara da cewa za su kara yawan jami’an da zasu rika kula da wuraren da sauran su daga ranar 17 ga watan Disamba tare da sanya na’urorin daukar hoto da na motsi, don rigakafin kai hari da bayar da cin hanci da rashawa.
“Saboda haka babu wata riba da za a ce ana sa ran zirga-zirgar zai karu a jihar da kashi 30% a wannan lokacin bukukuwan.sannan sn gano wasu mahimman wuraren da zasufi yawan cunkoson ababen hawa su ne cikin birinin Onitsha da titunan Onitsha- Owerri, Ihiala, Umunze, Awka metro, Amansea, Oye-agu junction / Abagana, Nnobi junction da Eke Awka.Umurnin ya shirya tsaf don magance waɗannan ƙalubalen zirga-zirgar dake tasowa.inda tuni muka sanya wasu dabarun aiki a wurin.
“Sun hada da tsawaita lokacin aikinmu, da kuma matsa lamba kan hukumomin da abin ya shafa don ci gaba da gyare-gyare a kan manyan ramuka da suka lalace a hanya.
Kazalika Kwamandan sashin, yayin da yake yabawa hukumomin tsaro da abin ya shafa da gwamnatin jihar Anambra bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa da tsaro cikin walwala, amma ya bukaci masu ababen hawa da sauran jama’a dasu hada kai a duk lokutan bukukuwa da sauran su.