Anambra: Ƴan Bindiga sun kashe Sojoji 2, sun ƙona Sakatariya, Kotu, Motoci 32
Ƴan bindiga a Jahar Anambra tsakanin ranakun Lahadi da Litinin, bayan sun kashe Sojoji biyu, sun sace Ɗan Majalisa, sun kuma ƙona Sakatariyar Ƙaramar Hukuma, ofishin rarraba wutar lantarki na Enugu, kotun Majistare, da kuma Ababen hawa sama da 32.
Hare-haren na zuwa ne, ƙasa da kwanaki 3, bayan Gwamnan Jahar Farfesa Chukwuma Soludo ya ziyarci Shugaban Ƙungiyar Tsagerun Biafra Nnamdi Kanu a magarƙamar sashen Jami’an tsaro na Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Magance Matsalolin tsaro, Talauci a Arewa —Wata Ƙungiya ga Manyan Arewa
Ƴan bindigar sun kashe ɗan Bigilanti a ranar Lahadi a yankin Eke Oko a Ƙaramar Hukumar Aguata.
Wanda lamarin ya faru dashi ya kasance yana sanye da rigar Mobayil a lokacin da suka Harbe shi.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Tochukwu Ikenga yace ƴan sanda sun ɗauko gawar shi.
” Bincike ne da akayi ya nuna cewa ashe wanda suka Harben ba Ɗan Sanda bane, kuma har yanzu ba’a gano shi ba,” Inji shi.
Ƴan bindigar sun kuma yiwa Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa ƙawanya dake Ogidi, a daren tare da ƙona Sakatariyar Ƙarama da Kotun Majistare dake cikin Sakatariyar.
Majiyoyi sun ce ƴan bindigar sun ƙona dukkanin kundi da Dukiyoyin na ƙaramar hukumar.
Sama da Motoci 32 da aka ajiye a wajen Ƙaramar Hukumar suma duk sun ƙone su.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan ya alaƙanta wannan lamari da ta’addanci.
Haka zalika sun je ofishin rarraba wutar lantarki na Enugu kusa da Sakatariyar tare da ƙone ta.
Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban Sadarwa na Ƙamfanin Mr. Emeka Ezeh ya bayyana rashin jindaɗi na wanna lamari, yana mai cewa duk ƙoƙarin su na kiran Hukumar kashe Gobara ta Jahar yaci tura.
Comments 1