By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya yi Allah wadai da kisan dan majalisa mai wakiltar mazabar Aguata II a majalisar dokokin jihar Okechukwu Okoye.
An yi garkuwa da Okoye da mai taimaka masa, Cyril Chiegboka a lokacin da suke dawowa daga aiki a ranar Lahadin da ta gabata.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai Christian Aburime, ya bayyana a matsayin “marasa zuciya” da “jahilci”, kisan gillar da aka yi wa dan majalisar.
Gwamnan ya ce cikin rashin kunya da bakin ciki ne labarin kisan ya zo masa.
Ya kuma jajanta wa ‘yan uwan wanda abin ya shafa a Isuofia, yana mai cewa mai yiwuwa ’yan kungiyar masu laifin ne suka kai masa hari tare da kashe ‘yan sanda uku a Isuofia shekaru biyu da suka wuce wanda kuma ke kan gaba.
Ya ce, “Amma ba za su taba iya kashe Isuofia da jihar Anambra ba.”
Soludo ya tabbatar wa Ndi Anambra kudurin gwamnati tare da sabunta kudurin da jami’an tsaro ke yi na ganin an hukunta masu laifin da kuma tabbatar da an gurfanar da su a gaban kuliya.
Gwamnan ya kuma bayar da tukuicin Naira miliyan 10m ga duk wanda ko kungiyar da za ta yi amfani da muhimman bayanai da za su kai ga cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika cikin gaggawa, yana mai tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba Anambra za ta zama jahannama ga masu aikata laifuka.
Sanarwar ta kara da cewa, “Anambra za ta yi nasara a kan dakarun duhu. Yakamata Ndi Anambra su jajirce wajen yaki da masu aikata laifuka.
“Har yanzu dai gwamnan yana cikin kaduwa dangane da ta’asar da aka yi wa ‘yan uwansa guda biyu, yana mai shan alwashin cewa dole ne a gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika, da kuma duk masu aikata laifuka a Anambra.
Comments 1