Daga: Abbas Yakubu Yaura
Al’ummar karkarar Eka Utara da ke Adani, cikin karamar hukumar Uzo-Uwani ta Jihar Enugu, sun shiga rudani sakamakon wani abin ban mamaki na mutuwar wani ango da wasu baki shida da suka halarci daurin aure a ranar Asabar.
Vanguard ta tattaro cewa wasu biyar, ciki har da amaryar, suma suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba a cikin al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Edo @ 31: Gwamna Obaseki Ya Nemi Tallafin Al’ummar Jihar Don Ci Gaba Da Gyare-gyaren Hukumomi
An kuma tattaro cewa wadanda iftila’in ya afkwa sun dawo ne daga wani daurin aure a Obollo-Afor da ke karamar hukumar Udenu a jihar Enugu a lokacin da suka fara mutuwa.
Wata majiya a yankin Adani da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Vanguard cewa suna zargin abincin da suka ci yana dauke guba.
Majiyar ta kuma ce wasu mutanen na zargin cewa wadanda abin ya shafa sun mutu ne sakamakon gurbatacciyar iskar shaka ta hayakin injin Janareta mai samar da wutar lantarki, wanda aka kawo a barandar gidan wadanda abin ya shafa suka sauka a lokacin da ake ruwan sama a lokacin da suka dawo daga bikin daurin auren.
Majiyar ta ce za a tabbatar da ainihin musabbabin mutuwar idan aka gudanar da bincike kan gawarwakin mutanen.
Majiyar ta ce: “Na samu labarin cewa wadanda abin ya shafa din, wadanda suka dawo daga Obollo-Afor inda suka halarci wani daurin aure, sun fara mutuwa ne ta ban mamaki.”
Hakazalika an gaya mani cewa wannan bangaran mace-macen na iya kasancewa sanadiyyar gubar abinci yayin da wasu ke cewa ta yiwu hayakin janareta ne ya haddasa shi, wanda aka kai shi barandar wani gida da suka sauka a lokacin da ake ruwan sama.
“Har ila yau, akwai zargin cewa bakin sun mutu ne sakamakon wani maganin kashe kwari, wanda aka fesa domin kawar da sauro a dakin.”
“Gaskiya muna cikin rudani yanzu. Binciken gawarwakin ne kawai zai tabbatar da abin da ya kashe su.”
Majiyar Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa wani makwabci ne, wanda ya je karbar sabuwar amaryar ne ya lura da yadda wadanda lamarin ya rutsa da su ke kwance a kasa, ya kuma sanar da wasu da suka hada kai wajen kai su asibiti.
Ko da yake mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Enugu, Daniel Ndukwe, bai iya tabbatar da rahoton ba, saboda ya shaida wa manema labarai cewa yana hidimar coci, daya daga cikin likitocin da ya karbi wasu daga cikin wadanda abin ya shafa a asibitinsa ya tabbatar da cewa biyar daga cikinsu sun mutu a wurinsa.
Ya ce “ba zai iya tantance hakikanin adadin wadanda suka mutu ba saboda wasu da lamarin ya shafa sun mutu a wasu asibitoci.”
A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Cafke Masu Kaiwa ‘Yan Bindiga Bayanan Sirri
Jami’an rundunar Sufeto-Janar na ‘yan sanda IGP da na IRT sun kama wasu masu ba da labari ga wata kungiyar masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, wadda ta yi garkuwa da matar aure da ’ya’yan wani dan majalisa, Hon.Dr Ibrahim Aminu, a jihar Katsina.
IRT ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar ta fitar a ranar Lahadi, 28 ga watan Agusta, 2022.