Gwamnatin Angola ta dakatar da biyan albashin likitoci sama da 5,000, inda ta bayyana yajin aikin da suka yi a matsayin Wanda ya sabawa doka.
Kungiyar likitocin kasar Angola ta fara yajin aiki na Sai baba ya gani ne a fadin kasar a makon da ya gabata domin matsa kaimi wajen ganin an samar da karin albashi da yanayin aiki.
Tsayar da ayyukan kiwon lafiyar jama’a ya gurgunta, kodayake wasu likitocin suna ba da agajin gaggawa.
Likitoci sun ce baya ga rashin albashi, cibiyoyin kiwon lafiya na fama da karancin kayan aiki da magunguna akai-akai.
Yajin aikin dai shi ne na biyu cikin watanni hudu. A watan Disamba, likitoci sun dauki matakin kan mutuwar yara 20 a wani asibiti da ke Luanda babban birnin kasar.
Likitoci sun yi zargin sun mutu ne saboda karancin magunguna da kayan aikin jinya.
Tattaunawar baya-bayan nan da gwamnati Bai yi nasara ba, bayan da likitocin suka ki amincewa da karin albashin kashi 6%.