Hukumar Tsara Birane ta Jahar Zamfara ta sanya Sakatariyar Jami’iyyar PDP da sauran gine-gine a matsayin basa kan ƙa’ida, kuma zata rushe su.
Dayake jawabi ga Manema labaru, Mai magana da yawun Mataimakin Gwamnan Jahar Umar Aminu Gusau, ya bayyana kaɗuwar sa na sanya ginin jami’iyyar a matsayin wanda baya kan ƙa’ida, inda ya bayyana buƙatar sa na tsaida rushe sakatariyar.
Yayi zargin cewa, an sanya sakatariyar a jerin wanda basa kan ƙa’ida sabudda bambancin siyasa a jahar, inda yace Gwamnatin yanzu bata son abokanan hamayya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan bindiga sun nemi Miliyan 100 kuɗin fansar Ɗalibar BUK da suka sace a Kano
A cewar sa, shuwagabannin PDP a jahar sun rubuta takarda ya zuwa hukumar tsara birane, da Kwamishinan ƴan sanda, da sashen jami’an tsaro na Sibil difens, da SSS da sauran hukumomin tsaro, a matsayin su san da takardar kafin su fara fentin sakatariyar.
“Hukumar tsara birane ta jahar bazata iya cewa ba’a sanar da hukumar kafin a fara fentin sakatariyar ba. Mun san cewa wannan shine ikon mulki” inji shi.
Gusau ya bayyana cewa a lokacin tsohon Gwamnan Jahar Abdu’aziz Yari ke jagorantar jahar, an baiwa PDP damar gudanar da harkokin ta, ba tare da cutarwa ba, amma Gwamnatin APC ta yanzu bata san wata jam’iyya ta riƙa ƙalubalantar ta.
A lokacin da aka tambaye shi akan matakin da zasu ɗauka nan gaba jahar, Gusau yace shuwagabancin Jami’iyyar na jiran martanin Mataimakin Gwamnan jihar Barista Mahadi Aliyu Gusau, wanda shine shugaban jam’iyyar a jahar.
A lokacin da aka so jin ta bakin shi a ranar Alhamis, Darkta-Janar na Hukumar Tsara Birane ta Jahar Zamfara Idris Garba Rikiji yace zaiyi jawabi ga Manema Labaru akan lamarin.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewar, har yanzu ƴan jarida na a farfajiyar Hukumar suna jiran Darkta-Janar yayi jawabi kamar yadda ya alƙawurta, amma shiru.
Comments 1