Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken zai fara wata ziyarar aiki ta farko a kasashen Afrika da suka haɗar da Najeriya, Kenya Senegal, a mako mai zuwa.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce Blinken zai kuma gana da shugabannin kasashen tare da bayyana musu manufofin kasar Amurka a kan yankin Africa.
Kazalika a yayin da ya ziyarci Kenya ana saka ran zasu tattauna batutuwan da suka shafi yankin, da kuma matsalar tsaro da makwabtan kasar ke fama da ita, irin su Somalia da Sudan.
Kazalika ana saka ran tattaunawar za ta tabo batutuwan da suka shafi annobar Corona da kuma sauyin yanayi.